Wednesday, 9 January 2019

ZAMA DAN SOSHIYAL MIDIYAN GWAMNATIN ZAMFARA, KO BANNAR SUNA!


Gwamnati tunbin giwa, ba mai iyawa da ke sai Allah. Wasu na ganin cewa muddun kana tare da gwamnati, kuna dasawa. Shi kenan Kai ka taka dahir.

Sai dai kash! Ba haka abun ya ke ba a jahar Zamfara. Hujja a nan ita ce;

A wannan duniyar ba wani Abu da ya ke muhimmanci a bangaren Jagoranci, kamar karfin kafafen yada LABARAI. Hakan ya sa kowace kasa ta ke ta kokarin Samar da kafar watsa LABARAI mai Karfi domin samun damar mulkar duniya!

Hasalima karfin kafar yada LABARAI ya fi na makamin Kare dangi....

Hakan ya sa kasashe da gwamnatocin da su ka San abunda su ke yi, sukan baiwa kafafensu muhimmanci fiye da kima.

Sai dai kash!

Ba haka abun ya ke ba a jahar Zamfara, duk da duk wani jami'in gwamnati Mai tunanen kirki da ilimin wayewar zamani ya San irin gudunmawar da kafafen Sada zumunta su ke takawa fiye da duk wata kafar watsa LABARAI mallakar jahar Zamfara, dama mazauniya jahar.

Amma ba wani tallafi na Azo a gani da ita gwamnatin ta baiwa masu taimaka mata wannan bangaren. Sai dai tarin bakin jini da bacin suna da kullum su ke tattarawa kawunansu!

Muna online tun kafin kafuwar gwamnati Mai ci a yanzu. Duk wani Wanda ya wahala a cikin wannan Gwamnatin tun 2010 zuwa yau ba daya da gwamnatin jahar ta taimaka, Hasalima wadanda su ka wahala tun farko ba daya da bai gaji ya ba baya ba. Wadanda su ka matso yanzu suna cikin wahala da ba ni hasashen za a yi masu abun da ba a yi masu baya ba.

Dan haka 'yan uwa yan soshiyal midiya, ya kamata mu yi wa kanmu kiyamullaili. Mu San Inda gari ya yi Muna Dan Hausawa sun ce da hasara gwamma, aikin kishiya.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

9-1-2019

Tuesday, 1 January 2019

AN SAKI SUMMAYA, TA TABBATAR DA GABANTA AKA KASHE SURAJO!

Alhamdulillahi Bayan kashe watanni biyu da kwana 7 cikin iyawar Allah an sako SUMMAYA BAYAN an biya naira Miliyan 10.


In dai ba ku manta ba ranar 24 ga watan 10 ne aka yi garkuwa da Sumayya tare da su hassana da Husaina da wasu yara biyu da kuma wani matashi Mai suna SURAJO. Sai dai an sako su Hassana da Husaina Bayan an biya naira Miliyan 15 haka su. Haka daga baya aka sako su yaran kanana Bayan an biya kudin fansa. Inda aka cigaba da tsare ita Sumayya da Surajo Wanda kwanakin baya suna bayar da kwana biyu in ba a ba su abunda su ke so ba su KASHE su. Sai Allah Allah bai nufi sun kashe Sumayya ba. Sai dai ita Sumayya ta tabbatar da a gaban idanunta aka KASHE shi Surajo.

Wednesday, 5 December 2018

BARAYIN SHANU SUN KASHE 'YAN SANDA 16 A JIHAR ZAMFARA.

'Yan sandan Najeriya sun ce jami'ansu goma sha shida ne suka mutu a jihar Zamfara bayan wata arangama da suka yi da barayin shanu a karamar hukumar Birnin Magaji ranar Alhamis din da ta gaba.

Wata sanarwa da rundunar 'yan sandan ta fitar ta ce ta ceto 'yan sanda 20 daga hannun barayin shanun, sannan ta kashe barayi 104. 

Sanarwar, wacce kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu, ya aike wa manema labarai ranar Talata da daddare ta kara da cewa jami'an tsaron sun kuma rusa sansanoni uku na barayin, sannan suka kwato shanu sama da 500 da akuyoyi 79.

"An aike da jiragen helikwafta uku wadanda suka kaddamar da hare-hare a maboyar barayin shanu da sauran 'yan fashi da makami da zummar kawar da gyauron su. Kazalika an aike da jami'an 'yan sanda na musamman da wadanda ke yaki da ta'addanci da kuma wadanda ke yaki da 'yan fashi da makami jihar ta Zamfara," in ji sanarwar.

Lamarin dai ya faru ne da yammacin Alhamis din nan, yayin da jami'an 'yan sanda na musamman ke sintiri a cikin dazuzzukan jihar ta Zamfara domin zakulo barayin shanu da masu garkuwa da mutane da ke addabar sassan jihar da dama.

Haka kuma dakarun na musamman sun kama sama da mutum 85 da ake zargin gungun masu aikata miyagun laifuka ne a jihar.

Sanarwar ta ce an kuma kwato bindigogi kusan 80 da kuma wasu muggan makamai.

Sakamakon kwanton baunar dai rundunar 'yan sandan kasar ta tura babban mataimakin sufeto janar domin zama babban kwamandan dakarun na musamman.

Babban aikin kwamandan shi ne maido da zaman lafiya a duka fadin Zamfara.

RAHOTON BBC HAUSA 

Thursday, 29 November 2018

KOTU TA YANKE HUKUNCIN KISA GA WADANDA AKA SAMU DA LAIFIN JEFA AL'KUR'ANI MAI GIRMA MASAI A JAHAR ZAMFARAWata kotun Shari'ar Musulunci da ke zama a Gusau. Ta yankewa tsohon Shugaban Jam'iyar APC NA mazabar Sabon gari. Da wani mutun daya hukuncin KISA ta hanyar Datse Kansu da Takobi har su mutu.

Akan laifin da aka Kama su da shi na sanya yara biyu suna jefa AL'KUR'ANI Mai Tsalki a cikin Masai. Inda shi kuma yaro daya daga cikin yara biyu dinda aka Kama, aka bayar da umurnin Kai shi gidan marayu na zaman Shekara da uku da damar in ya tuba za a sake Bayan Shekaru ukun in kuma bai tuba ba za a Kai shi gidan Yari.

Haka zalika kotun Ta Wanke Shugaban Karamar hukumar Gusau da Kansilan Gundumar Sabon gari Gusau. Saboda ba a samu shedun da za su tabbatar da cewar su ke sanya wadanda ke jefa AL'KUR'ANI Masai din su ke sanya su ba.

Sai dai kotun ta baiwa wadanda aka samu da laifi damar daukaka Kara nan da wata daya (30)

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau. Daga harabar kotun da ke nan Unguwar Yarima Gusau

Featured post

WACE ROMUWA CE MATASHIN JAHAR ZAMFARA YA KE SHA, A GWAMNATIN GWAMNA ABDUL'AZIZU ABUBAKAR YARI??

Ranar 1 ga watan 11 ce ranar Matasa da kungiyar hada kan Afrika ta ware domin tunawa da manyan gobenta, tare da kokarin nemawa Matasan nat...